Rezime epizode
A wannan makon, majalisun dokokin jihohi 36 na Najeriya sun amince da kudirin kafa ƴansandan jihohi. Sai dai yayin da ake murnar wannan mataki, wasu na nuna fargabar cewa gwamnonin jihohi za su iya amfani da wannan runduna wajen musgunawa ƴan adawa.
A wannan makon, majalisun dokokin jihohi 36 na Najeriya sun amince da kudirin kafa ƴansandan jihohi. Sai dai yayin da ake murnar wannan mataki, wasu na nuna fargabar cewa gwamnonin jihohi za su iya amfani da wannan runduna wajen musgunawa ƴan adawa.
Epizode
Dandalin siyasa,shirin da ke kawo muku irin wainar da ake toyawa a fagen siyasa
SlušanoA wannan makon, majalisun dokokin jihohi 36 na Najeriya sun amince da kudirin kafa ƴansandan jihohi. Sai dai yayin da ake murnar wannan mataki, wasu na nuna fargabar cewa gwamnonin jihohi za su iya amfani da wannan runduna wajen musgunawa ƴan adawa.
INEC a Najeriya ta cire sunayen bogi, sama da milyan 1 da dubu 600
SlušanoA cikin shirin dandalin siyasa na yau, za mu ji cewa a yayin da ake cigaba da shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, ta bayyana cewa ta cire sunayen bogi, sama da miliyan 1 da dubu 600 daga rajistar masu zaɓe, bayan gano kura-kurai da wasu jami’anta suka tafka-------------
Ɗaukaka ƙara daga ADC za ta dakatar da hukuncin kotu kan Atiku da jam'iyyar?
SlušanoA cikin shirin namu na yau, za mu ji cewa Babbar Kotun Tarayya ta soke shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin Sanata David Mark, tare da dukkan matakan da ya samar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar a zaɓen 2027. Za mu ji martanin Nafiu Bala Gombe, wanda ya shigar da ƙarar, da kuma martanin tawagar Atiku.
ADC ta magantu kan ikirarin da APC ta yi cewa Tinubu ya nada goyan bayan Arewa
SlušanoA cikin shirinmu na yau tare da Michael Kuduson za mu yi waiwaye akan babban gangamin fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya wanda shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar a Kaduna,, inda shugabannin jam’iyyar suka yi ikirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da goyon bayan Arewa. Za mu kuma ji martanin jam’iyyar ADC kan wannan ikirari, musamman batun cewa sama da mutum miliyan ɗaya ne suka halarci gangamin. Latsa alamar sauti don sauraron karin bayani.....
Ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan zargin INEC da saɓawa dokar zaɓe
SlušanoShirin Dandalin Siyasa na wannan mako tare da Michael Kuduson ya yi duba kan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan zargin cewa Hukumar Zaɓen Najeriye, ta gaza wallafa rajistar masu zaɓe a intanet cikin wa’adin da dokar Zaɓe ta tanada. Sai dai hukumar ta ce ba ta karya doka ba. Latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....